让旅途体验更美好 味觉体验更美妙
Manzo Muhammad Al-Habib ?an ?Abdullahi (Sallallahu ?Alaihi wa Sallam).
Muhammad ?an Abdullahi ?an Abdul-Mu??alibi ?an Hashimi ?an Abdu-Manafi ?an ?usayyi ?an Kilabi, Sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam, (Harshen Larabci: Abūl-Qāsim Mu?ammad ibn ?Abd Allāh ibn ?Abd al-Mu??alib ibn Hāshim ibn ?Abd Manāf ibn Qusayy ibn Kilāb) nasabarsa ma?aukakiya tana tuqewa zuwa ga Annabi Ibrahim, alaihi salatu wassalam. Manzon Allah ne. Khataman-Nabiyyin da addinin Musulunci.
Mahaifiyarsa: Ita ce Aminatu (āminah) 'yar Wahbi ?an Abdu-Manaf ?an Zuhrata ?an Kilabi (Radhi Allahu anha). Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.
La?abinsa: Al-Mus?afa yana da sunaye da suka zo a cikin ?ur'ani Mai Girma kamar, Khataman-Nabiyyin, da Al-Ummi da Al-Muzzammil da Al-Muddassir da An-Nazir da Al-Mubin da Al-Karim da An-Nur da An-Ni?ima da Ar-Rahma da Al-?Abdu da Ar-Ra'uf da Ar-Rahim da Ash-Shahid da Al-Mubasshir da An-Nazir da Ad-Da'i da sauransu.
Tarihin haihuwarsa: 17 Rabi'ul Auwal Shekarar Giwa (571m) bisa mash'hurin zance gun Ahlul-Baiti (a.s), an ce, 12 ga watan da aka ambata.
Wurin haihuwarsa: Makkah.
Aikoshi: An aiko shi a Makkah 27 Rajab yana ?an shekara arba'in.
Koyarwarsa: Ya zo da daidaito tsakanin dukkan halitta da 'yan-uwantaka da rangwame na gaba ?aya ga wanda ya shiga musulunci, sa'annan ya kafa shari'a ma?aukakiya da dokoki na adalci da ya kar?o daga wajan Allah su kuma musulmi suka kar?a daga gare shi.
Mu'ujizozinsa: Mu'ujizarsa madauwamiya ita ce ?ur'ani amma wa?anda suka faru a farkon Musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makkah a ?oye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.
Hijirarsa: ya yi hijira daga Makkah zuwa Madinah a farkon watan Rabi'ul Auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.
Ya?o?insa: Allah ya yi wa Manzo izinin ya?ar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi ?auki ba da?i da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune: Badar- Uhud- Al-Khandak (Ahzab)- Khaibar- Hunaini.
Matansa: Khadijah (Hadiza) 'yar Khu?wailid (a.s) ita ce matarsa ta farko, amma sauran su ne: Saudatu 'yar Zam?a da ?A'isha 'yar Abubakr da Ghaziyya 'yar Dudan (Ummu Shariq) da Hafsa yar ?Umar da Ramla 'yar Abu Sufyan (Ummu Habibia) da Ummu Salama 'yar Abu Umayya da Zainab 'yar Jahash da Zainab 'yar Huzaima da Maimunah 'yar Al-Haris da Juwairiyya 'yar Al-Haris da Safiyya 'yar Huyayyi ?an Akhdabl (r.a).
'Ya'yansa: 1-?Abdullah 2-Al-Qasim 3-Ibrahim 4-Fa?ima/Fatimah (a.s) a wani ?aulin da Zainab da Ruqayya da Ummu Kulthum.
Ammominsa: Tara ne, su 'ya'yan ?Abdul-Mu??alib ne: Al-Haris da Zubair da Abu ?alib da Hamza da Al-Ghaidaq da Dirar Al-Muqawwam da Abu Lahab da ?Abbass.
Ammominsa mata: Su shida ne daga iyaye mata daban-daban su ne: Aminah da Ummu Hakima da Barra da Atiqa da Safiyya da Arwa. Wasiyyansa goma sha biyu ne, su ne: Amirul-Mu'minina Ali ?an Abi ?alib (a.s) da Hasan ?an ?Ali da Hussain ?an ?Ali da ?Aliyyu ?an Husaini da Muhammad ?an ?Ali da Ja?far ?an Muhammad da Musa ?an Ja?far da ?Ali ?an Musa da Muhammad ?an ?Ali da ?Ali ?an Muhammad da Alhassan ?an ?Ali da Muhammad ?an Hassan Mahadi (a.s).
Mai tsaron ?ofarsa: Anas ?an Malik.
Mawa?insa: Hassan ?an Sabit, da ?Abdullahi ?an Rawahata, da Ka'abu ?an Malik.
Mai kiran sallarsa: Bilal Al-Habashi da ?Abdullahi ?an Ummu Maktum da Sa?ad Al-Kirdi.
Tambarin zobensa: Muhammadur Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.
Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.
Tarihin wafatinsa: 28 Safar 11 H.
Wajan da ya yi wafati: Madinah.
Inda aka binne shi: Madinah a Masallaci Ma?aukaki Mai Alfarma. Ka sani cewa Muhammad (S.A.W) shi ne ?arshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa qiyama kuma ita ka?ai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ?arshen rayuwar duniya da lahira. Kamar yadda shi ka?ai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ?aya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (S.A.W) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (S.A.W): Shi ne Muhammad ?an ?Abdullah (S.A.W) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makkah ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan ?ollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).
Aiko Annabi Mai Daraja (S.A.W)
An aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da saqo a 27 ga Rajab bayan yana ?an shekara 40 yayin da Jibrilu (A.S) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makkah ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Ala?i . Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makkah a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sa?on Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta" .
A lokacin tunda mutanen Makkah mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka ri?a yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni" . Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane ?alilan, na farkonsu Imam ?Ali sannan sai matarsa Khadijah (A.S) sannan sai wasu mutane. Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali sannan daga mata sai Hadiza (A.S).
Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madinah wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai qarfinsu ya da?u kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa Mai Sau?i Mai Hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madinah har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wa?anda ba na sama ba. Kuma an samu ya?o?i masu yawa a Madinah kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga ma?iya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana za?ar ?angaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wa?anda ake kashewa daga ?angarorin biyu ba su da yawa a dukkan ya?o?insa tamanin da wani abu, wato; wa?anda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ?aya da ?ari hu?u ba.
Mutuwa Mai Zafin Gaske Tun lokacin da aka aiko Annabi da sa?o har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (A.S) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin ?ur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (S.A.W) ya yi umarni da a ha?a shi kamar yadda yake a yau ?in nan. Manzo (S.A.W) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.